Wasu 'yan Najeriya na caccakar ma'aikatan wutar lantarki kan yajin aiki
Wasu 'yan Najeriya, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, sun harzuka sakamakon matakin da ma'aikatan wutar lantarkin kasar suka dauka na tafiya yajin aiki. Sun fara yajin aikin ne ta hanyar hana shiga da fita a hedikwatar kamfanin dillancin wutar lantarkin na Najeriya TCN a Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da safe. Sun kashe makunnan lantarki a ofisoshin da ke faɗin ƙasar, domin bijire wa umarnin da hukumar da ke sanya ido kan harkokin wutar lantarki ta bayar ga wasu shugabannin riko domin yin jarrabawar karin girma. A watan sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar ma'aikatan wutar lantarki, Mista Joe Ajaero ya sanya wa hannu ya umarci dukkan ma'aikatan wutar lantarki su yi zanga-zanga a hedikwatar ma'aikatar wutar lantarki da rassanta da ke fadin kasar saboda umarnin cewa dole su yi "jarrabawar karin girma." Ma'aikatan kamfanin dillancin lantarkin na son a dakatar da tsarin aikin da ake bi na ci gaban ma'aikata. Mista Ajaero ya kar...