Rashin ƴan takarar Kujerar Sanata na APC a Yobe da Akwa Ibom ...

 Sanata kuma shugaban APC Abdullahi Adamu ya ce ko kaɗan Jam'iyyarsu ta APC ba za ta sake ta yi asarar takarar sanata a mazaɓar Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta arewa-maso-yamma ba, inda hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta ce APC ba ta da ƴan takara.

Ya ce ba zai yi tsokaci kan batun ba saboda yana gaban kotu.

A makon jiya ne INEC ta bayyana cewa APC ba ta da masu takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

A cewar INEC, APC ta dora sunayen Sanata Ahmad Lawan da Godswill Akpabio cikin jerin sunayen 'yan takara a shafin intanet na INEC sai dai hukumar zaben ta yanke cewa mutanen biyu ba su aka tsayar ba a zaben fitar da gwanin Jam'iyyar.

Comments