NLC ta bukaci shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ƙara al'bashin ma'aikatan Kasar
Ƙungiyar kwadago ta NLC a Kasar ta nemi federal Government da ta kara albashin ma'aikatan kasar da kashi 50 cikin 100 lura da yanayin tsadar rayuwa.
Kungiyar ta mika wannan bukata ga shugaban qasar Muhammadu Buhari ta wasikar da ke dauke da sa hannun shugabanta Ayuba Wabba.
Sakon ya yi tuni da cewa gwamnonin su suka yadda da batun janye tallafin man fetur, da kawo batun ritayan ma'aikatan gwamnati a shekara hamsin, da kuma rage kudaden da ake bai wa majaliasa domin aikin wa 'yan qasa.
Ƙungiyar ta zargi gwamnoni kan wadannan shawarwari, su na mai cewa duk wanda ya yadda da ra'ayinsu to shi makiyin gwamnati.
Kungiyar ta ce akan karin albashi ne abin da ya fi a mayar da hankali a kai, domin a yanzu shi ne mafi muhimmanci.
Masu fafutikar dai na ganin akwai bukatar gwamnati take amfani da yanayin kasa da abubuwan da ke faruwa wajen fayyace salary da samawa 'yan kasar sauki rayuwa.
.jpg)
Comments
Post a Comment