Jam'iyar APC ce za ta ci zaben 2023 duk da matsalar tsaro a Najeriya - Abdullahi Adamu
Shugaban Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce suna da tabbacin samun nasara a babban zaɓen 2023 mai zuwa duk da tarin ƙalubalen da ƙasar ke ciki musamman matsalar tsaro da tsadan rayuwa.
Tsohon Sanata kuma shugaban jam'iyar APC Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa irin waɗannan matsalolin, musamman rashin tsaro, ba kawai a Najeriya ake fuskantar su ba har ma da wasu ƙasashen duniya.
Ya bayyana cewa "Ba shakka akwai lalacewar tattalin arziki a ƙasa, amma mai hankali ya san cewa lalacewar darajar naira ba wai mu muka haddasa ta a nan ba, batun rashin tsaro kuma babu wata ƙasa da za ka ce tana zaman lafiya."
Najeriya dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da ƙaruwar matsalolin rashin tsaro a sassan ƙasar.
A cewarsa, Jam'iyyar APC na aiki ne domin samun nasara a zaɓen da ke tafe sai dai ya ce akwai mutanen da ba ƴan jam'iyyarsu ba da suke musu zagon ƙasa kan wannan ƙudirin nasu.
Sai dai ya ce duk da haka gwamnati na kokarin na ganin an magance matsalolin.

Comments
Post a Comment