Zaben A Kenya: Raila Odinga da William Ruto na tafiya kai da kai Rohoto


 A yayin da aka kammala kidaya kusan rabin kuri'un da aka jefa a zaɓen shugabancin ƙasar Kenya, manyan 'yan takarar biyu na tafiya dai dai.

Mataimakin shugaban kasa, William Ruto ya ɗan bai wa tsohon firaminista Raila Odinga tazara kasa da - kashi 51 da 48 cikin 100.

Shugaban hukumar zaɓe na kasar ya ce tabbas ana samun jira wajen kidaya kuri'un.

Sau da dama ana tsayawa da kidaya kuri'a biyo bayan korafe-korafe daga magoya bayan jam'iyyu.

A ranar Asabar, magoya bayan Mista Odinga sun farwa wani yankin da jami'an zaɓe ke aiki, tare da zarginsu da cuta.

Yayinda su kuma magoya bayan Mista Ruto ke zargin cewa ana coge a harkokin kidaya kuri'u

An dai tsaurara tsaro na raba jami'an kwantar da tarzoma a kowanne yanki na kasar.

Kawo yanzu dai an tabbatar da gama kidaya kuri'un mazabu 141 cikin 292.

Kuma an bai wa kafofin yada labarai bayanai kan sakamakon wucin-gadi na wadannan mazabu, wanda ke nuna 'yan takarar biyu na tafiya kusa kusa..

Kusan sama da mutum miliyan 14 ne suka fita zabe.

Comments