Matar da za a ka ɗaure shekara 34 saboda sukar gwamnatin Saudiyya
Jami'ar Leeds da ke Saudiya ta bayyana damuwa kan yadda aka yanke wa ɗaya daga cikin ɗalibanta da ke digiri na uku hukuncin ɗaurin shekara 34 a gidan yari saboda wallafa wasu saƙonnin Twiter da a ciki ta zagii gwmanatin Saudiyya.
An cafke Salma al-Shehab, mai shekara 34 wadda take karatu a jami'ar leeds ta saudiya, wadda ƴar Saudiyya ce kuma tana da yara biyu a 2021 a lokacin da take hutu a ƙasar.
Kafin zuwa hutun, ta nemi a samar da sauye-sauye a kuma saki wasu masu fafutuka da ke daure a kurkukun Saudiyya.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun ce hukuncin mai tsauri ya nuna shakku kan iƙirarin Saudiyya na inganta haƙƙin mata kuma ya nuna yadda lamarin ke ƙara lalacewa.
Wata kotu da ke hukunta laifukan ta'addanci ta samu Shebab da laifin taimaka wa ƴan adawa wajen ta da hargitsi da yaɗa jita-jita, a cewar ƙungigoyin.
Sun ce shi ne hukunci mafi yawa da aka taɓa yanke wa wani mai fafutuka a ƙasar da ke yankin Gulf inda Yarima Mohammed Ibn Salman ke sa ido kan murƙushe ƴan adawa tsawon shekara biyar.
Shehab, wadda ɗaya ce daga tsirarun ƴan Shi'a a ƙasar da ƴan Sunni suka fi yawa, a shafinta na Instagram, ta bayyana kanta a matsayin ƙwararriya a fannin kula da tsaftar haƙori kuma mai wayar da kai kan lafiya.
Ta ce tana digirinta na uku a Jami'ar Leeds kuma tana koyarwa a Jami'ar Princess Nourah a Riyadh.
Rabon da a ga Shehab ta wallafa sabon saƙo a shafinta na Tuwita, da ke da mabiya 2,700, tun 12 ga watan Janairun 2021, kwana uku kafin aka ba da rahoton tsare ta a Saudiyya.
A ƙarshen watan da ya gabata, ta wallafa saƙonni da dama inda ta nemi a kawo sauye-sauye a Saudiyya sannan kuma a saki wasu fitattun masu fafutuka da malamai da wasu masana.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amurka mai suna The Freedom House da takwrarta ta Burtaniya ALQST sun rawaito cewa da farko an yanke wa Shehab ɗaurin shekara shida bayan samunta da laifin take dokokin ƙasar da suka shafi yaƙi da ta'addanci da laifukan intanet cikin ƙarshen shekarar da ta gabata.
A ranar 9 ga watan Agusta ne, wata kotun ɗaukaka ƙara ta tsawaita yawan shekarun da aka yanke mata zuwa 34 tare da ƙaƙaba mata takunkumin tafiye-tafiye na tsawon shekara 34 wanda zai fara aiki da zarar an sake ta, kamar yadda suka faɗa.
Bethany Al-Haidari, jami'in da ke lura da ƙarar a Kungiyar Freedom Initiative, ya soki hukuncin da aka yanke mata.
"Saudiyya dai ta sha iƙirarin inganta haƙƙoƙin mata da kuma aiwatar da wasu sauye-sauye a fannin shari'a. Amma ganin wannan hukunci, babu tantama cewa lamarin yana ƙara ƙazancewa ne," kamar yadda ta shaida a shirin Newshour na BBC da aka yi ranar Asabar.
"Mun kuma samu wasu rahotanni da ke cewa akwai daruruwan matasa mata da aka tsare su a tsukin lokacin da aka tsare Salma."
Shugabar yada labarai ta Ƙungiyar ALQST, Lina al-Hathloul, ƴar uwa ga Loujain al-Hathloul, ta bayyana ranar Litinin cewa hukuncin ya nuna hukumomin Saudiyya na kan bakarsu ta hukunta duk wanda ya bayyana ra'ayinsa ba tare da fargaba ba.
A ranar Laraba ne, wani mai magana da yawun Jami'ar Leeds ya faɗa wa BBC cewa: "Mun damu matuƙa game da batun baya-bayan nan kan shari'ar Salma kuma muna neman shawara kan ko akwai wani abu da za mu iya don tsaya mata." "Muna tare da Salma da iyalinta da ƙawayenta da sauran abokan karatunta."
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana nazari kan ƙarar Shehab kuma bai kamata a ɗauki mataki kan amfani da ƴancin faɗin albarkacin baki wajen nemawa mata ƴanci ba".
Zuwa yanzu dai gwmnatin Saudiyya ba ta ce komai ba kan rahotannin.

Comments
Post a Comment