Buhari ya sake naɗa Bashir Ahmad mataimaki na musamman
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kuma Kara naɗa tsohon mai ba shi shawara, Bashir Ahmad, a matsayin mataimaki na musamman kan kafofin sadarwa na zamani.
Kamfanin yada labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya tabbatar da naɗin cikin wata wasiƙa da ya aika wa Bashir mai kwanan wata 20 ga Yuli.
A cikin wasiƙar, Mr Mustapha ya ce naɗin ya fara aiki ne tun ranar 19 ga watan na Yuli.
Bashir ya sauka daga muƙaminsa na mai ba wa shugaban ƙasa shawara sakamakon umarnin da fadar gwamnatin ta bai wa masu son neman takara a zaɓen 2023 da su ajiye muƙaman nasu.
Sai dai matashin ɗan asalin Jihar Kano ya yi rashin nasara a zaɓen fitar da gwani a ƙarƙashin jam'iyyarsu ta APC mai mulkin Najeriya, inda ya nemi takararar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu daga Kano State.
Bashir ya ce an yi maguɗi a zaɓen fidda gonin kuma ya bayyana cewa ya kai ƙara kotu don a bi masa haƙƙinsa.
.jpg)
Comments
Post a Comment