Dan takarar Senator a jam'iyar APC a Jigawa ya rasu

 

Tijjani Ibrahim Gaya, dan  APC da ke takarar sanata a Kudu maso Yammacin Jigawa, ya rasu.

Ya rasu a  asibiti a China a jiya Asabar.

Rahotanni na cewa sai da aka soma kwantar da shi a wani asibiti da ke Abuja bayan gano cewa yana da cutar huhu kafin daga bisani a fitar da shi zuwa China domin samun cikakkiyar kulawa.

Watanni uku kenan da marigayin ya lashe primaries fitar da gwani.

Gwamna Jigawa, Muhamamdu Badaru Abubakar, ya ce wannan babban rashi ne a garesu a wata sanarwar ta'aziya zuwa ga iyalansa.

Marigayin ya taba wakiltar mazabarsa ta Dutse/Kiyawa a majalisar wakilai tsakanin 2011 zuwa 2015.

Comments

Popular posts from this blog

Wagila: Yadda ake hada bindigogi domin tunkarar 'yan fashin daji a Sokoto

Rashin ƴan takarar Kujerar Sanata na APC a Yobe da Akwa Ibom ...

Abu biyar da za a iya sa yara su yi a lokacin hutun makaranta madadin zaman banza