Abu biyar da za a iya sa yara su yi a lokacin hutun makaranta madadin zaman banza
A yayin da makarantun firamare da sakandari ke shiga watan dogon hutu, abin da ke damun iyaye shi ne yadda ‘ya’yansu za su amfana da wannan hutun ba tare da zaman banza ba.
Masu bincike sun bayyana matakan da suka kamata iyaye su dauka a irin wannan lokaci domin ganin ‘ya’yansu sun mori hutun.
Mamu Alhaji Muhammad, mai makarantar firamare ce da ke Abuja, kuma ya yi mana bayani a kan abubuwa da iyaye za su iya taimaka wa yaransu ba tare da dogon nazari ba.
Daga cikin abubuwan da ya yi nazari a kai akwai
Manhajar koyon karatu
Akwai karantarwa ta hanyar manhajoji da ake kira ‘Adaptive Learning System’, inda iyaye za su iya amfani manhajar a wayoyinsu ko kwamfutar hannu da yin rajista. Daya daga cikin manhajojin akwai ‘Youlesson’.
YouLeason: Wata manhaja ce da iyaye za su iya saukewa a wayoyinsu ko a kwamfutar hannu ko kwamfutar tebur.
Sai su yi rajistar yaransu inda za a ba wa ko wane yaro damar koyon darasi daga wurin malami kai-tsaye ta hanyar bidiyo, yaro na kallon malami, malami na kallon yaro.
Kuma iyaye za su iya zama a gefe suna lura da darasin da yaransu ke daukawa.
Mimo: Wannan manhajar na koyar da yara dabarun sarrafa kwamfuta (Computer Coding) ta yadda za su iya kirkiran manhaja da kansu.
Da kuma yadda za su fahimci harshe da kamfuta ke amfani:
Abubuwan da ba su shafi darussan aji ba:
Yara sun dade suna zuwa makaranta, yanzu da ake hutu, akwai bukatar ba su hutu daga abubuwan da suka shafi makaranta da daukar darasi.
Akwai abubuwa da dama da iyaye za su iya yi da yaransu domin shakatawa da kuma kara sabo tsakanin iyaye da ‘ya’ya.
Lokacin da yara ke zuwa makarantu, wasu iyayen kuma na zuwa wuraren aiki, wannan wata dama ce da wasu iyayen za su samu domin samun lokaci mai muhimmanci da ‘ya’yansu.
Alhaji Muhammad ya bayyana mana abubuwa da zai iya kara shakuwa tsakinin iyaye da yara ko kuma tsakanin ‘yan uwa. Daga cikinsu akwai:
· Ninkaya
· Ziyartar wurin shakatawa
· Kwallon kafa
· Wasan ‘yar-ɓuya
· Langa
· Carrafke
Ga iyaye masu hazaka kuwa za su iya yin wasan dambe ko kuma wasan doki da yaran nasu.

Comments
Post a Comment