Rigima kan ƴan takara Musulmai
Tsohon Sanata Abdullahi Adamu ya ce batun haɗa ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimaki duka Musulmai abu ne da yake ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce sai dai ya ce suna fatan ƙara ƙaimi wajen janyo ra'ayin ƴan ƙasar ga amincewa da wannan zaɓi.
Ya ce zai yi wuya a iya shawo kan al'ummar ƙasar kan wannan haɗi saboda "an samu wani hali ne a ƙasar da ko me ka ce, akwai waɗanda suka lashi takobin ba za su yarda ba kuma ba yadda ka iya da su" amma tun da ana kan tsarin dimokraɗiyya ne, kowa yana da ikon ya riƙe ra'ayinsa.
Ya bayyana cewa Ubangiji ne kaɗai ya san abin da ya sa mutane da dama suka yarda a zuciyarsu cewa haɗin Musulmi da Musulmi shi ne alheri a halin da ƙasar ke ciki.
Shugaban na jam'iyyar APC ya ce abu ne mai wahala ka iya samun goyon bayan jama'a ɗari bisa ɗari kan wani ƙudiri a don haka abin da za su fi mayar da hankali a kai shi ne yadda za su gamsar da ƴan ƙasar kan tsarin takarar Musulmi da Musulmi.
Comments
Post a Comment