Abin da ya sa ake yawan Rigima kan wajen da za a binne shugabannin Afirka


José Eduardo da ya mutu a watan da ya gabata, ya shafe sama shekara 38 a kan mulki kafin ya sauka a 2017.

Cikin jerin saqon nin  wasiƙun da muke samu daga 'yan jaridar Afirka, 'yar kasar Ghana Elizabeth Ohene ta yi rubutu game da irin taqaddamar da ake yi kafin binne shugabannin Afirka.

Ba  tabbacin ko zan iya ba da wani  zance, amma ni ban taɓa sanin cewa kasancewar mutum shugaban wata ƙasa a Afirka zai iya haddasa rigima a ƙabarinsa ba idan ya mutu.

Na yi ta bin rigimar da ake yi game da inda za a binne tsohon Shugaban Ƙasar Angola José Eduardo dos Santos, wanda ya mutu a Sifaniya ranar 8 ga watan Yuli.

Shugaban ƙasar mai-ci João Lourenço da kuma mai dakin sa Dos Santos na son a mayar da gawarsa gida don yi mata jana'izar ban-girma a ƙasaitacciyar maƙabarta ta musamman - abin da muke gani na girmamawa ga shugabanni a Ghana.

Amma 'yarsa mai suna Welwitschia "Tchizé" na son a yi masa jana'iza a killace kuma a binne shi a wani ƙabari na musamman a Sifaniya ta yadda su 'ya'yansa za su iya ziyartarsa.

Ta ce wasu daga cikin 'yan uwanta na goyon bayan burin nata, waɗanda ke fuskantar zargin cin hanci kuma za a iya kama su da zarar sun ziyarci a Angola.

Ɗaya daga cikin 'ya'yan Dos Santos ya ce ba ƙasar ce ke da alhakin ɗaukar nauyin jana'izarsa ba kuma iyalinsa ne ya kamata su yanke yadda za a yi.

Maganar cewa ko ƙasa na da iko kan gawar shugabanta ba yanzu aka fara ba.

An samu shigen wannan lamari a Zimbabwe a 2019 lokacin da Robert Mugabe ya mutu shekara kusan biyu da suka wuce bayan ya shekara 37 a kan mulki - inda shugaba mai-ci Emmerson Mnangagwa ya kawo ƙarshen mulkin nasa tare da goyon bayan sojoji.

Kowa ya yi tunani za a bine shi ne a Filin Gwaraza na Ƙasa ( Heroes' Acre) da ke garin Harare.

Ko ma dai mene ne, shi ne ya gina Heroes' Acre kuma ya binne da yawa daga cikin abokan sa, ciki har da Sally matarsa ta farko.

Mista Mnangagwa ya fara gina ƙabari na musamman don binne jagoran neman 'yancin, amma kuma iyalansa ba su amince da hakan ba ganin yadda aka kore shi daga mulki kuma abokan gwagwarmyarsa suka yi halin ko inkula shi.

Bayan shafe makonni ana taƙaddama, iyalinsa sun yi nasara kuma an binne Mista Mugabe, jagora kuma gwarzo a Zimbabwe, a ƙauyensu ba tare da wani wakilin gwamnati ba.

Hatta Kenneth Kaunda - shugaban ƙasa na farko bayan 'yancin kai a Zambia kuma ɗaya daga cikin 'yan  neman 'yanci - bai iya samun wurin da za a binne shi ba ba tare da rigima ba.

Iyalinsa su ka ce, ya so a binne shi kusa da matarsa da ta fara mutuwa ba inda gwamnati ta tanada ba.

Zuwa yanzu dai iyalin nasa ba su yi wata rikici ba yayin da "KK" - kamar yadda ake kiran sa da shi - na ci gaba da kwanciya Embassy Memorial Park da ke Lusaka baban birnin ƙasar.


 

Comments