Mohammad Abacha ye na son INEC ta tabbatar da takararsa ta gwamna a Kanon Dabo
Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar PDP, Mohammed Abacha ya nemi kotun Tarayya a Kano ta tilastawa hukumar zaɓe ta INEC tabbatar da shi dan takara ne.
Abacha ya qi yadda da hukuncin da ya tabbatar da cewa Sadiq Wali ne ɗan takarar PDP na Kano.
Mohammed Abacha ya ce shi ne ya lashe zaben fitar da gwamni da aka gudanar a ranar 25 ga watan May wanda ya ce INEC ta tura wakilai domin gani da ido, amma sai kuma aka chanza sunansa da Sadiq Wali.
Mai neman takarar na son kotu ta hana PDP da shugaban jam'iyyar na Kano gabatar da Wali a babban zaben da ke tafe a 2023.
Akwai dai rarabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP da ke da tsagi biyu a Kano.
Wannan dalilin ne ya sa bangarorin da ke rikici da juna kowa ya gabatar da na shi zaben fitar da gwanin.
Abin da ya kai ga PDP ta samu 'yan takara biyu kafin daga bisani aka tabbatar wa da Sadiq Wali kujerar takara.
Sai dai Mohammed Abacha tun daga wannan lokaci ya ke kalubalantar matsayar jam'iyyar da maka batun a gaban kotu.
A cikin watan Satumba za a cigaba da sauraron karar.
.jpg)
Comments
Post a Comment