Posts

Wasu 'yan Najeriya na caccakar ma'aikatan wutar lantarki kan yajin aiki

Image
  Wasu 'yan Najeriya, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, sun harzuka sakamakon matakin da ma'aikatan wutar lantarkin kasar suka dauka na tafiya yajin aiki. Sun fara yajin aikin ne ta hanyar hana shiga da fita a hedikwatar kamfanin dillancin wutar lantarkin na Najeriya TCN a Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da safe. Sun kashe makunnan lantarki a ofisoshin da ke faɗin ƙasar, domin bijire wa umarnin da hukumar da ke sanya ido kan harkokin wutar lantarki ta bayar ga wasu shugabannin riko domin yin jarrabawar karin girma. A watan sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar ma'aikatan wutar lantarki, Mista Joe Ajaero ya sanya wa hannu ya umarci dukkan ma'aikatan wutar lantarki su yi zanga-zanga a hedikwatar ma'aikatar wutar lantarki da rassanta da ke fadin kasar saboda umarnin cewa dole su yi "jarrabawar karin girma." Ma'aikatan kamfanin dillancin lantarkin na son a dakatar da tsarin aikin da ake bi na ci gaban ma'aikata. Mista Ajaero ya kar...

Matar da za a ka ɗaure shekara 34 saboda sukar gwamnatin Saudiyya

Image
  Jami'ar Leeds da ke Saudiya ta bayyana damuwa kan yadda aka yanke wa ɗaya daga cikin ɗalibanta da ke digiri na uku hukuncin ɗaurin shekara 34 a gidan yari saboda wallafa wasu saƙonnin Twiter da a ciki ta zagii gwmanatin Saudiyya. An cafke Salma al-Shehab, mai shekara 34 wadda take karatu a jami'ar leeds ta saudiya, wadda ƴar Saudiyya ce kuma tana da yara biyu a 2021 a lokacin da take hutu a ƙasar. Kafin zuwa hutun, ta nemi a samar da sauye-sauye a kuma saki wasu masu fafutuka da ke daure a kurkukun Saudiyya. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun ce hukuncin mai tsauri ya nuna shakku kan iƙirarin Saudiyya na inganta haƙƙin mata kuma ya nuna yadda lamarin ke ƙara lalacewa. Wata kotu da ke hukunta laifukan ta'addanci ta samu Shebab da laifin taimaka wa ƴan adawa wajen ta da hargitsi da yaɗa jita-jita, a cewar ƙungigoyin. Sun ce shi ne hukunci mafi yawa da aka taɓa yanke wa wani mai fafutuka a ƙasar da ke yankin Gulf inda Yarima Mohammed Ibn Salman ke sa ido kan murƙushe ƴan a...

Rashin ƴan takarar Kujerar Sanata na APC a Yobe da Akwa Ibom ...

  Sanata kuma shugaban APC Abdullahi Adamu ya ce ko kaɗan Jam'iyyarsu ta APC ba za ta sake ta yi asarar takarar sanata a mazaɓar Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta arewa-maso-yamma ba, inda hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta ce APC ba ta da ƴan takara. Ya ce ba zai yi tsokaci kan batun ba saboda yana gaban kotu. A makon jiya ne INEC ta bayyana cewa APC ba ta da masu takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma. A cewar INEC, APC ta dora sunayen Sanata Ahmad Lawan da Godswill Akpabio cikin jerin sunayen 'yan takara a shafin intanet na INEC sai dai hukumar zaben ta yanke cewa mutanen biyu ba su aka tsayar ba a zaben fitar da gwanin Jam'iyyar.

Rigima kan ƴan takara Musulmai

 Tsohon  Sanata Abdullahi Adamu ya ce batun haɗa ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimaki duka Musulmai abu ne da yake ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce sai dai ya ce suna fatan ƙara ƙaimi wajen janyo ra'ayin ƴan ƙasar ga amincewa da wannan zaɓi. Ya ce zai yi wuya a iya shawo kan al'ummar ƙasar kan wannan haɗi saboda "an samu wani hali ne a ƙasar da ko me ka ce, akwai waɗanda suka lashi takobin ba za su yarda ba kuma ba yadda ka iya da su" amma tun da ana kan tsarin dimokraɗiyya ne, kowa yana da ikon ya riƙe ra'ayinsa. APC: Shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu ya ce ya ɗauki alhakin matsalolin da ta shiga Taƙaddama tsakanin CAN da limaman Kirista kan halartar taron APC Ya bayyana cewa Ubangiji ne kaɗai ya san abin da ya sa mutane da dama suka yarda a zuciyarsu cewa haɗin Musulmi da Musulmi shi ne alheri a halin da ƙasar ke ciki. Shugaban na jam'iyyar APC ya ce abu ne mai wahala ka iya samun goyon bayan jama'a ɗari bisa ɗari kan wani ƙudiri a don haka abin da za...

Jam'iyar APC ce za ta ci zaben 2023 duk da matsalar tsaro a Najeriya - Abdullahi Adamu

Image
  Shugaban Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce suna da tabbacin samun nasara a babban zaɓen 2023 mai zuwa duk da tarin ƙalubalen da ƙasar ke ciki musamman matsalar tsaro da tsadan rayuwa.  Tsohon Sanata kuma shugaban jam'iyar APC Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa irin waɗannan matsalolin, musamman rashin tsaro, ba kawai a Najeriya ake fuskantar su ba har ma da wasu ƙasashen  duniya. Ya bayyana cewa "Ba shakka akwai lalacewar tattalin arziki a ƙasa, amma mai hankali ya san cewa lalacewar darajar naira ba wai mu muka haddasa ta a nan ba, batun rashin tsaro kuma babu wata ƙasa da za ka ce tana zaman lafiya." Najeriya dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da ƙaruwar matsalolin rashin tsaro a sassan ƙasar. A cewarsa, Jam'iyyar APC na aiki ne domin samun nasara a zaɓen da ke tafe sai dai ya ce akwai mutanen da ba ƴan jam'iyyarsu ba da suke musu zagon ƙasa kan wannan ƙudirin nasu. Sai dai ya ce duk da haka gwamnati na kokarin na ganin an magance matsalolin.

Buhari ya sake naɗa Bashir Ahmad mataimaki na musamman

Image
  Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kuma Kara naɗa tsohon mai ba shi shawara, Bashir Ahmad, a matsayin mataimaki na musamman kan kafofin sadarwa na zamani. Kamfanin yada labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya tabbatar da naɗin cikin wata wasiƙa da ya aika wa Bashir mai kwanan wata 20 ga Yuli. A cikin wasiƙar, Mr Mustapha ya ce naɗin ya fara aiki ne tun ranar 19 ga watan na Yuli. Bashir ya sauka daga muƙaminsa na mai ba wa shugaban ƙasa shawara sakamakon umarnin da fadar gwamnatin ta bai wa masu son neman takara a zaɓen 2023 da su ajiye muƙaman nasu. Sai dai matashin ɗan asalin Jihar Kano ya yi rashin nasara a zaɓen fitar da gwani a ƙarƙashin jam'iyyarsu ta APC mai mulkin Najeriya, inda ya nemi takararar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu daga Kano State. Bashir ya ce an yi maguɗi a zaɓen fidda gonin kuma ya bayyana cewa ya kai ƙara kotu don a bi masa haƙƙinsa.

Dan takarar Senator a jam'iyar APC a Jigawa ya rasu

Image
  Tijjani Ibrahim Gaya, dan  APC da ke takarar sanata a Kudu maso Yammacin Jigawa, ya rasu. Ya rasu a  asibiti a China a jiya Asabar. Rahotanni na cewa sai da aka soma kwantar da shi a wani asibiti da ke Abuja bayan gano cewa yana da cutar huhu kafin daga bisani a fitar da shi zuwa China domin samun cikakkiyar kulawa. Watanni uku kenan da marigayin ya lashe primaries fitar da gwani. Gwamna Jigawa, Muhamamdu Badaru Abubakar, ya ce wannan babban rashi ne a garesu a wata sanarwar ta'aziya zuwa ga iyalansa. Marigayin ya taba wakiltar mazabarsa ta Dutse/Kiyawa a majalisar wakilai tsakanin 2011 zuwa 2015.