Wagila: Yadda ake hada bindigogi domin tunkarar 'yan fashin daji a Sokoto
Da alamu al'ummomin yakunan karkara a sahar arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba amsa kiran da wasu mahukunta suka yi na su yi tattalin makamai domin kare kansu daga harin ‘yan bindiga saboda yadda abin ke wuce gona da iri.
A yayin wata ziyara da ya kai a wasu yankuna a jihar Sakkwato kwanakin baya, maaikacin bbc hausa Haruna Shehu – Tangaza ya lura da yadda mutane musamman ‘yan banga ke tanadar wata naui na bindigar gargajiya mai hadarin gaske da ake kira "wagila" domin kare yankunan su.
Kan haka ne ma ya samu zantawa da daya daga cikinsu wanda ya fi son a bayyana shi da kawai Sarkin Bindiga yayin da shi ma ya samo tasa wagilar.
Comments
Post a Comment