'Yan Funtua da kewaye na Qarafi kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga

 



'Yan garin Funtua da kewaye da ke a jihar Katsina  Najeriya na qorafi game da yawaitar haraharen da ƴan bindiga ke kaiwa a yankin, waɗanda kuma suke satar mutane domin neman kudin fansa.

A cewar wasu daga cikin Mutanen yankin, tun ƴan bindiga suna musu ɗauki ɗai-ɗai, yanzu lamarin ya baci, saboda a ranar Alhamis ɗin da ta wuce kusan mutum goma aka kwashe a lokaci daya.

Mazauna kewayen birnin na Funtua sun bayyana cewa ƴan bindiga sun saka su a gaba inda suke kai masu hari suna garkuwa da mutane.

Jama'ar garin sun ce tun suna tsammanin samun sauki zuwa wani lokaci, lamarin sai ta'azzara yake yi har ta kai ga wasu ala tilas sun fice daga Gidajen su.

Wani d'an yankin na Funtua ya ce akwai wasu ƙauyuka da ke kewayen Funtua wadanda tuni suka watse saboda bala'in ƴan bindiga.

Ya  ce akwai wasu ƙauyuka  irin su Zagamawa, su ma jama'ar garin duk sun tashi, sai dai jama'ar garin su je cikin Funtua su kwana da safe kuma su koma.

 ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta ce tana da labarin abubuwan da ke faruwa a Funtua da kewaye amma ta ce jami'anta na iya kokarin su wajen ɗaukar mataki.

Shugaban rundunar SP Gambo Isa ya bayyana cewa sakamakon yadda daji ke kara duhu a lokacin damina, dama ƴan bindiga na yawaita hare-haren su amma ya ce jami'ansu suna iyakar bakin kokarinsu.

Haka kuma Shugaban ƴan sandan ya bayyana cewa kwamshinan ƴan sandan jihar da kwamandojin sojoji da sauran hukumomin tsaro da ke jihar sun dage wajen hada kai tare da tsara dabarun tunkarar lamarin. Lamarin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a kewayen Funtuwa, har ta kai ga mutanen yankin sun fara zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu.

Comments